Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-28 15:56:35    
An cimma nasarar zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a Hefei

cri

An cimma nasarar yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing yau 28 ga wata a birnin Hefei na lardin Anhui dake kudu maso gabashin kasar Sin.

Da misalin karfe 8 na safiyar yau din nan ne, aka kaddamar da bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a cibiyar nune-nune da tarurruka ta kasa da kasa ta Anhui. Kafin kaddamar da bikin, daukacin mutanen wurin sun yi zaman makoki har na tsawon minti guda, domin nuna babban alhini ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.

Da misalin karfe 10 da rabi na safe, a dandamalin cibiyar wasannin motsa jiki ta birnin Hefei, wanda shi ne zangon karshe na bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics a Hefei, mai dauke da fitila na karshe Fan Xueping ya kunna tukunyar wutar gasar wasannin Olympics. Wannan dai ya alamanta cewar an kammala bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a Hefei tare da cikakkiyar nasara.

Tsawon hanyar da aka ratsa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Hefei ya kai kilomita kimanin 10.8, gaba daya dai akwai masu dauke da fitila 222 wadanda suka halarci bikin. An ratsa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a wasu shahararrun wuraren yawon shakatawa da gine-gine, ciki har da Huiyuan, da tafkin Tian'e.

Gobe wato ranar 29 ga wata, za'a zagaya da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Huainan da birnin Wuhu na lardin Anhui.(Murtala)