Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-28 09:43:38    
An soma bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Hefei

cri

Yau 28 ga wata din nan ne, aka kaddamar da bikin zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Hefei na lardin Anhui dake kudu maso gabashin kasar Sin.

Da misalin karfe 8 da safiyar yau ne, an yi bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a cibiyar nune-nune da tarurruka ta kasa da kasa ta Anhui. Kafin kaddamar da bikin, daukacin mutanen wurin sun yi zaman makoki har na tsawon minti guda, domin nuna babban alhini ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan.

Tsawon hanyar da aka ratsa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Hefei ya kai kilomita kimanin 10.8, gaba daya dai akwai masu dauke da fitila 222 wadanda suka halarci bikin. Za'a ratsa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a wasu shahararrun wuraren yawon shakatawa da gine-gine, ciki har da Huiyuan, da tafkin Tian'e. Za'a kammala bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing ne a dandamalin cibiyar wasannin motsa jiki ta birnin Hefei.(Murtala)