Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-28 07:43:02    
Kasar Sin tana kara karfafa aikin sarrafa magani mai sa kuzari

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, kasar Sin tana kara karfafa aikin sarrafa magani mai sa kuzari, sassan da abin ya shafa kamarsu hukumar binciken abinci da magani ta kasar Sin da babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin da ma'aikatar kiyaye kwanciyar hankali ta kasar Sin da sauransu sun yi bincike tare kan aikin hada maganin kara kuzari da na sayar da maganin da kuma na shigi da fici, kuma sun kai bugu ga wasu kamfanoni saboda sun yi aikin saba wa doka, ban da wannan kuma, sun yi kokarin kyautata aikin shigi da fici na maganin kara kuzari bisa doka. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.

Tun daga watan Oktoba na shekarar bara, sassa biyar na kasar Sin wato hukumar binciken abinci da magani ta kasar Sin da babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin da saura uku sun dauki matakai tare don kara kyautata aikin sarrafa maganin kara kuzari. Aiki mafi muhimmanci da suka yi shi ne sun bukaci a rubuta alamar "ya fi kyau a hana 'yan wasa su sha maganin" a kan dukkan magunguna masu kunshe da abu mai kara kuzari. Kazalika, hukumar binciken magani ta kasar Sin ta sanar da jerin sunayen magunguna dake kunshe da abun kara kuzari, wadannan magunguna sun hada da magunguna iri kusan dubu biyu. Kakakin watsa labarai na hukumar madam Yan Jiangying ta bayyana cewa, "Don hana 'yan wasa su yi kuskuren shan maganin kara kuzari, mun sanar da jerin sunayen magunguna masu kunshe da abun kara kuzari, kuma kamata ya yi a rubuta alamar 'ya fi kyau a hana 'yan wasa su sha maganin' kan takardun bayaninsu. Kuma daga ran 1 ga watan Mayu na bana, idan an tarar da irin wadannan magunguna ba tare da alamar ba, to, dole ne a hana a sayar da su a kantuna."

An yi mana bayani cewa, bayan kokarin da aka yi, an riga an hana kamfanoni 18 da su ci gaba da hada magani saboda sun saba wa doka. Ban da wannan kuma, an ci tarar kudi ga wasu kantunan sayar da magunguna saboda ba su bi doka ba.

Kazalika, kasar Sin ta tanadi cewa, dole ne kamfani ya yi shigi da fici na abun kara kuzari bayan da ya sami yarda daga wajen sashen da abin ya shafa na kasar Sin. Game da wannan, madam Yan Jiangying ta bayyana cewa, haka zai hana shigi da ficin abun kara kuzari ba bisa doka ba, kuma shi ne kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi don yaki da magani mai sa kuzari a duk fadin duniya. Ta ce: "Gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da iznin shirya gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing don kara karfafa aikin sarrafa maganin kara kuzari daga dukkan fannoni, kuma gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da iznin shirya gasar wasannin Olympic don kara kyautata aikin hada maganin kara kuzari da kuma sayar da shi, haka kuma za a kara tabbatar da lafiyar jama'ar kasa wajen yin amfani da magani. Shi ya sa za mu ci gaba da nuna kwazo da himma don yin nazari kan aikin binciken maganin kara kuzari cikin dogon lokaci, a karshe dai, za mu ba da babban amfani ga sha'anin yaki da magani mai sa kuzari na duniya."

Kan wannan, an yi mana bayani cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara ba da muhimmanci kan aikin kai bugu ga laifin bayar da labaran sayar da abun kara kuzari ta hanyar internet da kuma laifin sayar da abun kara kuzari ta hanyar internet. A sa'i daya kuma, sassan da abin ya shafa na kasar Sin za su kara binciken aikin shigi da fici na abun kara kuzari kuma za su kara kai bugu ga laifin fasa kwauri. (Jamila Zhou)