Dalilin da ya sa gasar wasannin Olympic ta zamanin da ta ci gaba cikin dogon lokaci yana da nasaba da tsarin zaman al'ummar kasar Greece ta da. A karni 5 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, zaman al'ummar bawa na kasar Greece ta da ya sami wadatuwa da ba a taba ganinta a da ba, gasar wasannin Olympic ta da ita ma ta sami habaka, amma, bayan wannan, musamman bayan yakin Peloponnesus da ya faru a karshen karni 5 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, sabanin dake cikin gidan kasar Greece ta da ya kara tsanani. A sanadiyar haka, zaman al'ummar bawa na kasar ya soma samun koma baya, a sa'i daya kuma, gasar wasannin Olympic ta zamanin da ita ma ta soma koma baya.
Yakin Peloponnessus ya faru ne tsakanin kawancen birane biyu na kasar Greece ta da, wato an yi yakin ne tsakanin kawancen Peloponnesus da kawancen Delian. Yakin ya fara ne daga shekarar 431 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, kuma ya gama ne a shekarar 404 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, wato shekaru 27 ke nan ana yin yakin. Yakin ya lahanta tattalin arzikin Greece sosai da sosai, har ya sa Greece ta koma baya a kai a kai.
Karni 5 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam lokaci mafi muhimmanci ne ga gasar wasannin Olympic ta zamanin da. Bisa tabarbarewar tattalin arziki da dagulewar halin zaman al'umma, ma'anar gasar wasanni ta canja, a da kuma, an bai wa 'yan wasa da suka ci nasara hular furanni kawai, amma a wancen lokaci kuwa, aka ba su dukiya da ikon musamman, a sanadiyar haka, 'yan wasan sana'a wadanda suka shiga gasar wasannin Olympic sun kara karuwa a kwana a tashi, wadannan 'yan wasan sana'a sun mayar da gasa a matsayin sana'arsu wato sun shiga gasar domin neman samun kudi kawai. A kai a kai, tunanin gasar wasannin Olympic ya canja.
A takaice dai, ana iya cewa, gasar wasannin Olympic ta zamanin da ta kara tabarbare musamman domin yaki da illar gasa, a sanadiyar haka, mutane ba su begen gasar kamar yadda suka yi a da ba, kuma ba su mai da hankali kan wasannin motsa jiki kamar yadda suka yi a da ba, halin almubazzarancin da gasar wasannin Olympic ta zamanin da ke ciki ya kara tsanani. Yayin da tsohuwar Roma ta mamaye Greece, sai gasar wasannin Olympic ta zamanin da ta kawo karshen tarihinta.(Jamila Zhou)
|