Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-27 20:33:44    
Ba a gano bullar munanan cututtuka masu yaduwa da al'amuran ba zata da za su kawo barazana ga lafiyar al'umma ba a wuraren da ke fama da girgizar kasa

cri

Ran 27 ga wata, a nan Beijing, Sun Jiahai, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai, a wuraren da ke fama da girgizar kasa ba a gano bullar munanan cututtuka masu yaduwa da kuma al'amuran ba zata da za su kawo barazana ga lafiyar al'umma ba.

Wannan kakaki ya kara da cewa, ko da yake girgizar kasar ta kawo illa ga tsarin ba da rahoto kan barkewar cututtuka masu yaduwa a wuraren da ke fama da girgizar kasar, amma hukumomin da abin ya shafa suna daukar matakan kara yawan ma'aikatan hana yaduwar annoba da gabatar da rahoto ta wayar salula domin tabbatar da ganin cewa, ana sa ido da kuma ba da rahoto kan barkewar annoba a dukkan gundumomi da garuruwan da ke fama da girgizar kasar da kuma wuraren tsugunar da wadanda suke fama da girgizar kasar. Yanzu hukumomin kiwon lafiya sun riga sun sami rahotanni kan wasu cututtuka masu yaduwa, amma ba a gano barkewar cututtuka masu yaduwa da al'amuran ba zata da za su kawo barazana ga lafiyar al'umma a wani wuri ba zato ba tsammani ba.(Tasallah)