Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-27 16:59:29    
'Yan kasar Rasha suna sha'awar kiwon lafiya bisa ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin a birnin Sanya

cri

Barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A 'yan shekarun nan da suka gabata, dimbin 'yan kasar Rasha suna sha'awar yin amfani da lokacin hutu na lokacin hunturu wajen zuwa birnin Sanya na lardin Hainan na kasar Sin. A idanunsu, ba kawai suna iya samun hasken rana da teku da rairayi da kuma idanun ruwa a birnin Sanya da ke yankunan zafi ba, har ma za su samu lafiyar jiki lokacin da suke kiwon lafiyarsu bisa ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wannan batu.

A asibitin ilmin likitanci na gargajiya na kasar Sin na birnin Sanya, Madam Alisha da ta zo daga kasar Rasha tana kwance tana cikin shirin samun jiyya da za a yi mata da allurar acupuncture.

Wakili: A ina ne kika zo?

Alisha: birnin Chita.

Wakili: Kin zo wurin domin samun jiyya kawai?

Alisha: E, haka ne, za a yi mana jiyya har kwanaki goma.

Wakilin: Daga ina ne kika san wannan dabarar kiwon lafiya bisa ilmin likitanci na gargajiya na kasar Sin?

Alisha: Wani dan kasar Rasha ya gaya mini, kuma masu ja-gora su ma sun gabatar da wannan.

Wakilin: Yaya ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin?

Alisha: Ilmin liktancin gargajiya na kasar Sin hanya ce mafi kyau wajen kiwon lafiya.

Kullum a kan yi amfani da hanyar motsa jiki da kuma magungunan tsire-tsire wajen yin jiyya bisa ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin, shi ya sa ba ta yi illa ga lafiyar jiki ba. Haka kuma tana ba da amfani sosai a fannonin kau da gajiya da daidaita tsarin kula da sassan jikin mutane. A shekara ta 2002, asibitin ilmin likitanci na gargajiya na kasar Sin na birnin Sanya ya fara hadin gwiwa tare da cibiyoyin ilmin likitancin gargajiya na kasashen waje domin hada kiwon lafiya bisa ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin tare da yin yawon shakatawa a yankunan zafi. Dimbin 'yan kasar Rasha masu yawon shakatawa sun zo birnin ta jirgin sama na musamman domin shan iska da safe da kuma samun jiyya bisa ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin da yamma, ta yadda suka ji dadin wannan hanyar kiwon lafiya sosai.

Wannan shi ne karo na biyu da Mr. Ivan da shekarunsa ya kai 58 da haihuwa ya zo birnin Sanya don yawon shakatawa. Kuma a ko wane karon da ya zo birnin, ya kan shiga asibitin ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin don samun jiyya. Kuma ya bayyana cewa, ta jiyyar da aka yi masa, zafin da ya ji a wuya da kuma bayansa ya samu sauki. Kuma ya kara da cewa, "A lokacin zafi, na kan sha aiki sosai, shi ya sa na kan zo birnin a lokacin hunturu. Na samu jiyya ne domin warkar da cutar wuya, kuma na ji mamaki sosai da amfanin ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin."

Cibiyar nishadi ta kiwon lafiya ta Heshengtang da ke birnin Sanya ita ce wata cibiyar kiwon lafiya da ta yi suna sosai ga 'yan kasar Rasha masu yawon shakatawa. Fadinta ya zarce murabba'in mita 5000, kuma an gayyaci nagartatun kwararru a fannin ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin daga duk fadin kasar don yin wa baki jiyya. Xu Ruohong, manaja na cibiyar ya gaya wa wakilinmu cewa, "A kan fi samun yawan 'yan kasar Rasha a farkon wata shekara a cikin ko wace cibiyar kiwon lafiya ta hanyar motsa jiki. Suna ba da gaskiya sosai ga ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin, shi ya sa su kan zo wurin don samun jiyya cikin lokaci a ko wace rana lokacin da suke birnin Sanya."