Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-27 17:18:15    
Girgizar kasa a Sichuan ba za ta yi illa ga gudanar da harkokin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin ba

cri

Jama'a masu sauraronmu, bar kanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yau na ' Mu leka Kasar Sin'. Ni Sani Wang ne a yau Talata ke gabatar muku da wannan shiri daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin.

Ko da yake bala'in girgizar kasa da ya auku a lardin Sichuan na kasar Sin ya haddasa mutuwar mutane masu tarin yawa yayin da sauran wassu suka jikkata da kuma babbar hasarar dukiyoyin jama'a, amma duk da haka, wassu kwararrun da abin ya shafa sun yi hasashen cewa, bala'in ba zai yi illa ga gudanar da harkokin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin daga dukkan fannoni ba, wato ke nan mummunar illa da bala'in zai yi a wassu fannoni ne kawai kuma cikin gajeren lokaci.

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, wannan babbar girgizar kasa mafi muni da ta auku a ran 12 ga wata a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ta kuma shafi birnin Chongqing da lardunan Shanxi, da Gansu, da Yunnan da kuma Guizhou da dai sauran wurare. Kawo yanzu dai, wannan bala'in ya rigaya ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 60,000 yayin da yake lalata muhimman ayyuka a fannin samar da lantarki, da sadarwa da kuma na hanyoyin mota ; Ban da wannan kuma kamfanoni da masana'antu fiye da 14,000 sun yi hasarar kudin Sin wato Yuan biliyan 67 sakamakon bala'in ; Dadin dadawa, shuke-shuke noma na dubban kadada sun samu barna daga bala'in.

Mr. Yi Xianrong, masanin nazarin harkokin kudi na kasar Sin ya furta cewa :" Ko da yake wannan babbar girgizar kasa ta janyo babbar hasara ga ayyukan bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, amma illa kadan bala'in zai yi saboda ya auku ne a wassu wurare kan tsaunuka na lardin Sichuan dake yammacin kasar Sin, inda mutane kalilan ne ke zaune wadanda suke samun rashin ci gaban tattalin arziki".

Jama'a masu sauraro, wassu mutane na shakkun cewa wannan bala'in girgizar kasa zai haddasa karin raguwar darajar kudi. Game da wannan dai, Mr. Yi ya dauka cewa, bala'in zai yi tasiri ne ga farashin kayan masarufi a wassu fannoni kawai kuma cikin gajeren lokaci.

An labarta cewa lardin Xichuan yana kan muhimmin matsayi a kasar Sin a fannin tsarin samar da amfanin gona, yawan albarkar noma da akan samu daga lardin ya dauki kashi 6 cikin kashi 100 bisa na duk kasa baki daya; Mr. Wei Chaoan, mataimakin ministan noma na kasar Sin ya furta cewa:" Ko da yake wannan bala'in girgizar kasa mafi muni ya janyo babbar hasara ga sha'anin noma na wuraren da bala'in ya shafa, amma a galibi dai yanayin aikin kawo barkar noma na duk kasa a wannan shekara yana da kyau; Farashin kayan noma na zauna da gindinsa. Lallai muna cike da imanin bada tabbaci ga samar da kayan abinci da kuma namun dabbobi kamar yadda ya kamata".

Aminai 'yan Afrika, a yanzu haka dai, gwamnatin kasar Sin ta riga ta sanya ayyukan sake gina gidaje da farfado da aikin kawo albarka a cikin ajandar ayyukanta. Gwamnatin tsakiya ta rigaya ta ware kudin Sin wato Yuan biliyan 70 wajen gudanar ayyukan bayan bala'in. Mr. Yi Xianrong ya furta cewa: " Zuba makudan kudade wajen ayyukan sake gidaje da farfado da aikin kawo albarka bayan bala'in, labuddah zai bada kwarin gwiwa ga bunkasa tattalin arzikin wuraren da bala'in ya shafa cikin sauri. Wassu mutane na kiyasta cewa yawan cigaban tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kashi biyu zuwa uku daga yunkurin sake gina gidaje da kuma farfado da aikin kawo albarka bayan bala'in". ( Sani Wang )