Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-27 15:06:53    
An yi bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara a birnin Nanjing

cri

Yau 27 ga wata din nan ne, aka cimma nasarar kammala bikin zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Nanjing dake gabashin kasar Sin.

Birnin Nanjing zango na karshe ne a lardin Jiangsu wajen zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Da misalin karfe 8 da minti 12 da safe, aka kaddamar da bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a cibiyar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Nanjing. A karshe ne, da misalin karfe 10 da rabi da safe, fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta isa lambun shan iska ta Gulou. Tsawon hanyar da aka ratsa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kai kilomita 12.9.

Akwai masu dauke da fitila 208 wadanda suka halarci bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing wanda aka shirya a birnin Nanjing, ciki har da 'yan sanda 2 wadanda suka kammala ayyukansu na yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane suka dawo nan ba da jimawa ba.

An shirya bikin nuna babban alhini kafin aka kaddamar da bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing, mutanen da suka halarci bikin yawo da fitilar sun nuna babban alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu a cikin bala'in girgizar kasa da ya fadawa gundumar Wenchuan.(Murtala)