Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 19:21:59    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin.

cri

---- Kwanan baya an kammala aikin fassara kundaye 83 na babban littafin addinin Budda na "Pattra-leaf Sutra", kuma an riga an buga da kuma sayar da kundaye 30 na farkon wannan babban littafi.

Littafin addinin Budda na "Pattra-leaf Sutra" wani irin wa'azi ne wanda aka rubuta ko sassaka kan wani irin ganyayen itacen da ake kira Pattra da ke jihohi masu zafi, kuma shi ne kayan addini mai daraja na tarihi na gundunar Xishuangbanna ta kabilar Dai mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin da sauran kasashe da shiyyoyi da yawa na kudancin Asiya da na kudu maso gabashin Asiya. Daga shekarar 2002, gwamnatin Xishuangbanna da cibiyar binciken al'adun Pattra-leaf na jami'ar Yunnan sun fara aikin "ceton al'adun kabilar Dai da ke kan ganyayen itatuwa", kuma sun fara aikin fassara da kuma buga kundaye 100 na babban littafin addinin Budda na "Pattra-leaf Sutra", da akwai masanan ilmi 'yan kabilar Dai da na 'yan kabilar Han da kuma manyan sufaye wadanda yawansu ya kai kusan 50 sun shiga wannan aiki.

---- Bayan da aka shafe shekaru 3 ana kokarin aiki, sai a watan Agusta na wannan shekarar da muke ciki, aka kammala dukkan ayyukan buga littafi mai suna "Takardu masu daraja na lokacin Xixia na kabilar Tibet na kasar Sin" wanda ya jawo hankulan mutane sosai. Mr. Bai Lichen, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya cire labulen da ke alamanta buga wannan babban littafi mai daraja. Kwararrun sun bayyana cewa, Wannan babban littafin da aka buga ya kammala aikin binciken ilmin Xixia na kasar Sin wanda a da a kasa yinsa, wanda kuma zai kara inganta matsayin kasar Sin a sassan ilmin kasashen duniya wajen ilmin Xixia.

Kwararru suna gani cewa, wannan littafi yana da ma'ana mai muhimmancin gaske wajen binciken dangantaka da kuma zaman jituwa da aka yi a zamanin da a tsakanin kabilun kasar Sin.

---- Bisa wani labarin da muka samu a ran 5 ga watan Nuwamba daga wajen ofishin binciken halittu masu rai na faffadan tsaunin da ke arewa maso yammacin kasar Sin an ce, karo na farko ne aka sami nasara wajen dasa irin saiwar tsime ta kabilar Tibet da ake kira Herba Swertiae Chirayitae a lardin Qinghai na kasar.

Bisa binciken da kwararru suka yi sun tabbatar da cewa, amfanin saiwar tsime mai suna Herba Swertiae Chirayitae da aka dasa ta hanyar dan adam ya fi na halitta wajen warkar da maras lafiya. Da haka ne kasar Sin ta samu fasahar dasa irin wannan saiwar tsime wanda a da ta kasa yinsa.

A da akan samu irin wannan saiwar tsime daga kasashen Indiya da Nepal, irin wannan saiwar tsime ta fi ba da taimako wajen warkar da masu ciwon hanta da matsarmama cikin likitancin kabilar Tibet. A shekarar 2002 an shigar da ita cikin sunayen kayayyakin likitancin da ke dab da karewa na duniya.