A ran 22 ga wata da yamma, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma firayin ministan kasar Sin, kuma babban jagora na babbar hedkwatar ba da jagoranci wajen yaki da girgizar kasa da gudanar da aikin ceto Mr. Wen Jiabao ya isa yankunan da aka yi girgizar kasa ta jirgin sama, domin jagorantar aikin yaki da girgizar kasa.
Da safiyar ranar 23 ga wata ne, firaminista Wen ya yi rangadi a yankuan Mianyang da kuma Deyang. Haka kuma, ya je makarantar sakandare ta Beichuan domin ganema idonsa kan halin da dalibai suke ciki wajen farfado da karatunsu.
A ran nan da yamma kuma, Mr. Wen ya isa birnin Pengzhou, domin yin rangadi kan halin da aikin ceto yake ciki a birnin. Ya ce, tabbas ne jama'a su gudanar da aikin yin rigakafin cututtuka yadda ya kamata, domin tabbatar da ganin ba a sami bullar wata babbar cuta bayan babbar girgizar kasa ba. Ya ci gaba da cewa, babban sakatare Hu Jintao ya shugabanci kamfanoni da yawa domin nuna goyon baya gare su. Ya yi imani cewa, sakamakon hakan, tabbas ne jama'ar kasar Sin za su samu nasara wajen yaki da girgizar kasa.(Danladi)
|