A 'yan kwanakin baya, kafofin watsa labaru na ketare sun bayar da bayanai bi da bi, inda suka yaba wa kasar Sin da ta gudanar da ayyukan ceto cikin sauri kuma yadda ya kamata wajen yaki da girgizar kasa, kuma tana da hangen nesa, da kuma tana bin ra'ayin mayar da babbar moriyar jama'a a gaban kome.
Jaridar 'Lianhe Zaobao' ta kasar Singapore ta bayar da wani bayani a ran 22 ga wata cewa, a yunkurin yaki da girgizar kasa, shugabannin kasar Sin sun dauki matakai cikin sauri, sun gudanar da ra'ayin mayar da babbar moriyar jama'a a gaban kome sosai da sosai, wannan ya kafa wani kyakkywan misalin gwamnatin kasar Sin a zuciyar 'yan siyasar kasashen yamma da kuma jama'arsu.
Ban da wannan kuma, jaridar 'El Espectador' ta kasar Colombia, da jaridar 'New Zealand Chinese Herald' ta kasar New Zealand, da kuma jaridar 'The Australian' ta kasar Australiya sun bayar da bayanai domin yaba wa ayyukan ceto da kasar Sin take gudanarwa wajen yaki da girgizar kasa.(Danladi)
|