Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 18:56:33    
Har ila yau ana cikin hali mai tsanani a lardin Sichun wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane

cri
A ran 23 ga wata, Mr. Li Chengyun, mataimakin shugaban lardin Sichuan na kasar Sin ya yi bayani a nan birnin Beijing kan sabon ci gaba da aka samu wajen halin da ake ciki sakamakon girgizar kasa da ta afka a gundumar Wenchuan da aikin ceto da kau da bala'in. Ya bayyana cewa, yawan hasarar da aka samu wajen rayukan mutane da dukiyoyi sabo da girgizar kasa da irin wahalar da ake sha domin yin ceto da kau da bala'in dukkansu ba safai akan ga irin su a tarihi ba, sabo da haka ana cikin hali mai tsanani wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane.

A ran 12 ga wannan wata, an yi girgizar kasa mai karfin digiri 8 a gundumar Wenchuan ta lardin Zichuan na kasar Sin, ya zuwa ran 22 ga wata da karfe 7 na yamma, yawan mutanen da suka mutu sakamakon bala'in ya wuce 55,000, sauran mutane fiye da dubu 280 sun jikkata, fadin wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa ya wuce murabba'in kilomita dubu 100, yawan mutanen da suke shan walahar bala'in kuma ya kai kusan miliyan 28. Mr. Li ya ce, "Jimlar sojojin 'yantar da kasa da sojoji 'yan sanda, da mutane 'yan kwana-kwana da 'yan sanda masu tsaro da kuma sojoji fararen hula da kasar Sin ta aika da su don yin ceto sun wuce dubu 140, yawan likitoci da masu aikin jiyya kuma ya kai 48,680, yawan mutane da aka kubutar da su daga kangaye kuma ya kai 83,988."

Mr. Li Chengyun ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu jimla kudin da lardin Sichuan ya ware domin ceton mutane daga bala'in ta kai kudin Sin wato Yuan biliyan 5.6, kuma ya ba da gudummawar kayayyaki da yawa ga jama'a masu fama da bala'in ciki har da tantuna da tufafi da abinci da ruwan sha da kuma magunguna. Ya zuwa yanzu, yawan jama'a masu fama da bala'in da aka tsugunar da su ya wuce miliyan 5.4, kowanensu yana iya samun taimakon kudi da abinci a kowace rana, marayu da tsofaffi maras dangi da nakasassu wadanda kuma kowanensu ya iya samun kudin Sin Yuan 600 a kowane wata domin zaman yau da kullum. Yanzu ana nan ana sake samar da kayayyaki daga kasuwannin yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa, farashin kayayyakin kuma yana zama yadda ya kamata.

Bisa kididdigar da aka yi ba cikakke ba an ce, girgizar kasar da ta afka wa gundumar Wenchuan kuma ta yi sanadiyar rushewa da lalacewar dakuna dubu dubai, miliyoyin mutane sun rasa gidajensu. Mr. Li ya bayyana cewa, har Ila yau ana cikin hali mai tsanani wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane. Ya ce, "Yanzu muna bukatar tantuna sosai domin yin ceto da ba da gudummawa ga mutane masu fama da bala'in, da akwai mutane da yawansu ya wuce miliyan 5 suna bukakar samun wurin kwana da kyau. Ban da wannan kuma muna bukatar na'urorin tsabtace muhalli ciki har motocin shara da na fesa ruwa. Muna bukatar su sosai"

Mr. Li Chengyun ya bayyana cewa, gwamnatocin da ke wuraren da bala'in ya shafa za su yi kokarin samar da gidajen kwana masu kyau kuma masu amfani cikin wata daya ga jama'a masu fama da bala'in da yawansu ya kai kashi 98 bisa 100, sa'an nan kuma za a samu tabbaci ga wadannan mutane wajen samun abinci da ruwan sha mai tsabta. Mr. Li ya ce, "Yanzu ana nan ana aikin farfado da wuraren da bala'in ya shafa. Ayyukan da muke yi suna hade da fannoni 3 wato na farko shi ne, tsara shiri, na 2, yin bincike, na 3 kuwa shi ne, za a yi sabon aikin daidaituwa wajen aikin kawo albarka na nan gaba bisa harsashin bala'in da ya faru a wannan gami." (Umaru)