Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 18:39:27    
An kawo karshen yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a rana ta farko a birnin Shanghai

cri

Yau 23 ga wata da yamma, an kawo karshen bikin yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a rana ta farko a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin.

Za a yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing har na kwanaki biyu daga ranar 23 zuwa ranar 24 ga wata a birnin Shanghai. An fara yawo da fitilar a ran nan da karfe 8 da safe, kafin a bude bikin, dukkan mahalartan bikin sun nuna ta'aziyya har na minti daya ga 'yan uwanmu da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan.

An fara bikin yawo da fitilar daga filin arewa na gidan ajiye kayan gargajiya na Shanghai, bayan haka kuma, an wuce wurin yin babban taron na jam'iyyar kwaminis ta Sin na farko, da sabon yanki mai suna "Pudong", da sauran shahararrun wuraren birnin Shanghai. A karshe dai, an cinna wutar kwanon wutar wasannin Olympic dake lambun shan iska mai suna "Lujiazui" dake gabar kogi.

A ranar 24 ga wata, za a cigaba da yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Shanghai. (Bilkisu)