Aminai 'yan Afrika, bayan aukuwar babban bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 12 ga watan da take tafe a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin,domin bada tabbaci ga samar da kayayyakin masarufi da na agaji ga wuraren da bala'in ya shafa, ma'aikata' kasuwanci ta kasar Sin ta kaddamar da shirin ko-ta-baci ba tare da bata lokaci ba don bada tabbaci sosai ga samar da kayayyaki ga kasuwannin wuraren da bala'in ya shafa. Hakan ya bada amfani mai yawa ga aikin samar da kayayyakin yayin da ake zaunar da farashin kayayyakin kasuwannin.
A gun taron ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kassar Sin da aka gudanar jiya Alhamis, ministan kasuwanci na kasar Sin Mr. Chen Deming ya bayyana cewa :' Bayan aukuwar wannan mummunar girgizar kasa, ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta kaddamar da shirin ko-ta-baci ba tare da bata lokaci ba domin tattara kayayyakin masarufi da na agaji ruwa a jallo. Muhimman abubuwa guda biyu da ma'aikatar take yi su ne, na farko : ana tattara kayayyaki daga dukkan fadin kasar domin bada tabbaci ga saye da sayarwa a kasuwannin wuraren da bala'in ya shafa ; Muhimmin aiki na biyu shi ne : ana kokarin farfado da shagunan kasuwanci tun da wuri.'
Sa'annan Mr. Chen ya furta cewa, a yanzu haka dai, ana iya samun kayayyaki yadda ake so daga kasuwannin birnin Chengdu, hedwatar lardin Sichuan da kuma sauran manyan biranen lardin. Muhimmin aiki da ake yi shi ne bude hanyoyin mota domin samar da hajjoji ga jama'ar da suka fi fama da bala'in a garuruwa da kauyuka.
Kazalika, Mr. Chen ya bayyana cewa, bisa matsayin tsananin bala'in, ma'aikatar kasuwanci ta kebe kauyuka kimanin 3,100 na wuraren da bala'in ya shafa da matsayin muhimman shagunan kasuwanci da za a farfado da su.
Jama'a masu saurare, a lokacin da ake sanya iyakacin kokari wajen bada tabbaci ga samun kayayyaki a kasuwannin wuraren da bala'in ya shafa, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin tana kuma daukar nauyin karbar tallafi daga gamayyar kasa da kasa. Shugaban sashen kuma da harkokin kasashen duniya na ma'aikatar Mr. Zhang Kening ya furta cewa: " A farkon farko na lokacin aukuwar mummunar bala'in girgizar kasa, mun kuwa yada labarin da abin ya shafa ga kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa da kuma hukumomin gwamnatocin kasashen waje da ke nan kasar Sin. Tun daga ran 13 ga wata dai, mun samu tallafin kudi da kuma sauran kayayayk irinsu kayan abinci da tantuna ,da maganguna da dai sauran kayayaykin makamantansu'.
Bugu da kari, ya furta cewa, a cikin aiki na gaba na farfadowa, ma'aikatar kasuwanci za ta kuma cigaba da yin hadin gwiwa tare da hukumomi masu bada tallafi na gamayyar kasa da kasa wajen gudanar da shirye-shiryen samar da kayayyaki da wasu ayyuka wadanda ake fi bukata a wuraren da bala'in ya shafa.
A gun taron watsa labarai, Mr. Chen Deming ya tabbatar da cewa: "Wannan mummunan bala'in girgizar kasa ya janwo babbar hasara ga jama'a a lardin Sichuan; amma bai kawo cikas sosai ga kasuwannin dukkan fadin kasar ba. Yanzu kasar Sin na da isassun adanannun kayan abinci, da man girki da kuma namu."
A karshe dai,Mr. Chen ya fayyace cewa,kawo yanzu, a galibi dai, bala'in girgizar kasa da ya auku a lardin Sichuan bai kawo tsaiko ga aikin fitar da kayayyaki kasar Sin zuwa ketare ba. ( Sani Wang )
|