Ran 23 ga wata, a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya yi, Mr. Li Chengyun mataimakin gwamnan lardin Sichuan ya ce, yanzu ana aiwatar da ingantaccen ayyukan fama da bala'i da ayyukan ceto da sauri yadda ya kamata.
Mr. Li Chengyun ya ce, hukumomin da abin ya shafa za su cigaba da kokarin neman wadanda ke da sauran numfashi, da fadada wuraren da ake yin ayyukan ceto, da kuma kara mai da hankali kan ba da agaji ga mutanen da suka jikkata, da fitar da wasu da ke cikinsu zuwa sauran larduna. A sa'i daya kuma, za a kokarin kwantar da mutanen da ke shan wahalar bala'in, ba da tabbaci wajen samar da abinci, da ingantaccen ruwan sha, da kuma kokarin samar da gidajen kwana ba na dindindin ba ga mutane kashi 98 cikin 100 wadanda ke shan wahalar bala'in cikin wata gadu.
|