Ran 23 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Li Chengyun mataimakin gwamnan lardin Sichuan ya ce, ya zuwa ran 22 ga wata da karfe 7 na yamma, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon bala'in girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ya kai 55,239, sauran mutane 281,066 sun jikkata, ban da haka kuma, mutane 24.949 sun bace.
A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mr. Li Chengyun ya ce, bayan da bala'in girgizar kasa ya faru, akwai sojojin fiye da dubu 140 da mutane masu ba da agaji kusan dubu 50 sun je wuraren da suke shan wahalar bala'I domin yin ayyukan ceto, yawan mutanen da aka tono su daga tarkacen gidajen da suka rushe ya kai kusan dubu 84.
Ban da haka kuma, Mr. Li Chengyun ya bayyana cewa, bisa kididdigar da aka yi, wannan bala'in girgizar kasar ya rushe ko lalata gidaje fiye da miliyan 10, milliyoyin mutane sun rasa gidajensu.
|