Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 12:26:08    
An fara mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Shanghai

cri

An fara aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing na kwanaki 2 a ran 23 ga wata da safe a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin.

A ran nan da karfe 8 da safe, an fara mika wutar wasannin Olympic a birnin Shanghai. Kafin a bude bikin fara mika wutar, dukkan mahalartan bikin sun nuna ta'aziyya ga 'yan uwanmu da suka rasa rayukansu a bala'in girgizar kasa na gundumar Wenchuan har minti daya.

Mai mika wutar yola ta farko ita ce Zhuang Yong da ta samu lambar zinariya a gasar yin iyo ba tare da shimfida ka'ida ba ta mata ta mita 100 a wasannin Olympic na Barcelona na shekarar 1992.

Yau, an fara mika wutar yola a filin arewa na gidan kayan gargajiya na Shanghai, masu mika wutar yola za su wuce wurin yin babban taron na jam'iyyar kwaminis ta Sin na farko, da sabon yanki mai suna "Pudong" da sauran shahararrun wuraren birnin Shanghai, a karshe dai, mataimakin mai ba da umurni ga tsarin kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane kirar Shenzhou Qing Wenbo zai cinna kwanon wutar wasannin Olympic dake lambun shan iska mai suna "Lujiazui" dake gabar kogi.(Lami)