Ran 23 ga wata, jaridar People's Daily da ake bugawa a nan birnin Beijing ta ba da bayyani cewa, yayin da mutanen kasar Sin suka yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane, gudummawa marasa son kai daga dukkan al'ummomin duniya sun yi kwararowa zuwa kasar Sin, jama'ar kasar Sin ba za ta manta da shi ba, kasar Sin ta nuna godiya ga dukkan duniya.
A cikin bayyanin, an bayyana cewa, a lokacin da kasar Sin take bukatar taimako ruwa a jallo, gamayyar kasa da kasa sun nuna babban juyayinsu ga bala'in girgizar kasa da ta fadawa a kasar Sin, kuma sun nuna alhini ga mutanen da suka rasu a sakamakon girgizar kasa, haka kuma sun nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arsu suka yi wajen ceton mutane.
A cikin bayyanin, an bayyana cewa, bala'in daga indallahi zai iya aukuwa a dukkan duniya, duk da ko wace kasa ta yi barna, gwamnatin kasar Sin da jama'arsu za su ci gaba da bayar da iyakacin kokarinsu ga mutanen da suka bukaci taimako.(Bako)
|