Ma'aikatar kudin kasar Sin ta bayar da wata sanarwa cikin gaugawa jiya 22 ga wata, inda ta bukaci sassan kula da kasafin kudi na matakai daban-daban da su inganta karfinsu wajen sa ido kan tallafin kudi da kayayyakin agaji na yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane, ta yadda za'a bada cikakken tabbaci ga tafiyar da ayyukan yaki da bala'in da ceto mutane daban-daban yadda ya kamata kuma daidai bisa tsari.
Ma'aikatar kudin Sin ta bukaci sassan kula da kasafin kudi na matakai daban-daban da su kara zuba kudi, da tattara kudade cikin himma da kwazo, da bada tabbaci ga zaman rayuwar mutanen da mummunan bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, da farfado da ayyukan samarwa, da sake gina gidaje ba tare da wani jinkiri ba. Hakazalika kuma, kamata ya yi a daidaita kudaden da aka tattara, da maida aikin ceto mutane masu fama da kangin talauci da mummunan bala'in girgizar kasa ya ritsa da su cikin gaugawa, da tsugunar da su yadda ya kamata a gaban kome, da yiwa mutane masu ji rauni jiyya, da yin rigakafin yaduwar cututtuka, da daidaita batutuwan matattu da aka samu bayan aukuwar mummunar girgizar kasa yadda ya kamata.
Bisa rahoton da ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar, an ce, zuwa karfe 12 da tsakar rana na jiya ranar 22 ga wata, gaba daya ne yawan kudin karo-karo da aka samu daga cikin gida da ketare ya kai kudin Sin Yuan biliyan 21.416.(Murtala)
|