Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-23 10:31:24    
Firaministan Sin ya bada umurni ga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane a garin Mianyang na lardin Sichuan

cri

Firaministan kasar Sin, kuma babban kwamandan babbar hedkwatar bada umurni ga aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin Wen Jiabao yana cigaba da shugabancin aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane yau 23 ga wata a garin Mianyang na lardin Sichuan.

Da safiyar yau din nan ne, firaminista Wen ya je asibitocin da abin ya shafa a garin Mianyang domin binciken yadda ake yiwa mutanen da suka ji rauni jinya. Haka kuma, ya je makarantar sakandare ta Beichuan domin ganema idonsa kan halin da dalibai suke ciki wajen farfado da karatunsu.

Yayin da firaminista Wen ke binciken halin da ake ciki a Mianyang, ya bayyana cewar, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta riga ta tura mutane masu fasaha guda 4500 domin gudanar da ayyukan kiwon lafiya da yin rigakafin annoba, ta yadda za'a tabbatar da cewar kada a samu mummunar yaduwar cututtuka bayan aukuwar mummunan bala'in girgizar kasa.(Murtala)