A cikin 'yan kwanakin nan, wasu shugabannin kasashen ketare da wakilan kungiyoyin kasa da kasa sun cigaba da zuwa ofisoshin jakadanci da karamin ofishin jakadanci na kasar Sin dake ketare da ofishin wakilan kasar Sin dake kungiyoyin kasa da kasa, domin nuna babban alhini ga mutane wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya rutsa da yankin Wenchuan na lardin Sichuan.
Firaminista Seyni Oumarou na Jamhuriyar Nijar ya je ofishin jakadancin Sin dake Nijar jiya 22 ga wata, inda ya nuna ta'aziyya ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunar girgizar kasa. Oumarou ya bayyana cewar, a madadin gwamnatin Nijar da jama'arta ne ya nuna matukar juyayi ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta, da nuna ta'aziyya ga mutanen da suka rasu.
Kazalika kuma, zaunanniyar tawagar kasar Sin a kungiyar kyautata ilimi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta kafa dakin nuna ta'aziyya a ofishinta daga ranar 19 ga wata zuwa ranar 21ga wata, inda jami'an kungiyar UNESCO da wakilan kasashen duniya daban-daban suka nuna babban alhini ga mutane wadanda suka rasa rayukansu.
A waje daya kuma, shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf da 'yan majalisar ministocin kasar, da firaminista Gyurcsany Ferenc na kasar Hungary, da firaministan gwamnatin kasar Czeck Mirek Topolanek, da shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Myong Bak, tare kuma da firaministan kasar Girka Costas Karamanlis su ma sun je ofishin jakadancin Sin dake kasashensu, domin nuna ta'aziyya ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa.(Murtala)
|