Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 22:00:13    
An kawo karshen yawo da fitilar wasannin Olympics a lardin Zhejiang

cri
Yau 22 ga wata, an kawo karshen bikin yawo da fitilar wasannin Olympics a biranen Ningbo, da Jiaxing da ke gabashin kasar Sin, wato ke nan an samu nasara wajen yawo da fitilar a lardin Zhejiang.

Domin nuna babban alhini ga mutane, wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa yankin Wenchuan na lardin Sichuan, bayan da aka yi shawarwari tare da kwamitin gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, an dakatar da bikin yawo da fitilar wasannin Olympics ta Beijing har kwanaki 3 daga ranar 19 ga wata zuwa ranar 21 ga wata.

Da karfe 7 na safiyar yau din nan ne, aka cigaba da yawo da fitilar wasannin Olympics ta Beijing. An yi yawo da fitilar ta hanyar babbar gada da ke hada gabobin teku ta Hangzhou, wato gadar da ke hada gabobin teku da ta fi girma a duniya, masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 118 sun halarci bikin.

A wannan rana da yamma, an cigaba da bikin a birnin Jiaxing, masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 90 sun halarci bikin.
A ranar 23 ga wata kuma, za a cigaba da bikin yawo da fitilar wasannin Olympics a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. (Bilkisu)