A ran 22 ga wata da yamma, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma firayin ministan kasar Sin, kuma babban jagora na babbar hedkwatar ba da jagoranci wajen yaki da girgizar kasa da gudanar da aikin ceto Mr. Wen Jiabao ya isa birnin Mianyang da jirgin sama, domin jagoranta aikin yaki da girgizar kasa.
Mr. Wen ya jaddada cewa, kwanaki 11 sun riga sun wuce bayan girgizar kasa, ya kamata jama'ar yankunan girgizar kasa su mayar da bakin ciki a matsayin karfinsu, su yi kokarin da suke iyawa, domin maido da ayyukan masana'antu da ayyukan gona da na kasuwanci, bisa tushen tabbatar da lafiyarsu.(Danladi)
|