Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 21:24:07    
Kasar Sin za ta yi gyara kan kasafin kudi na wannan shekara sakamakon girgizar kasa

cri

A ran 22 ga wata a birnin Beijing, shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Wu Bangguo ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi gyara kan kasafin kudi na wannan shekara sakamakon girgizar kasa, haka kuma kasar Sin za ta kaddamar da asusun daidaituwa na kasafin kudi na gwamnatin tsakiya, wanda ya zama babban sashe na kudin da za a yi amfani da shi wajen sake gina yankunan girgizar kasa.

Mr. Wu ya jaddada cewa, za a yi gyara kan kasafin kudi ne domin mayar da yaki da girgizar kasa da tabbatar da zaman rayuwar jama'a na yankunan girgizar kasa a matsayin wani aiki da ya fi muhimmanci, haka kuma za a ba da kudi da yawa da za a bukata kuma daga abubuwan hakika.

Mr. Wu ya ci gaba da cewa, ya kamata a tabbatar da kebe kudi cikin lokaci wajen yaki da girgizar kasa da sake gina yankunan girgizar kasa, da kuma kara duddubawa da sa ido kan yadda za a yi amfani da kudin.(Danladi)