Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 21:07:43    
Kasar Sin na fata da kuma maraba da kasashen duniya da su fi bayar da tantuna a yayin da suke ba da agaji, in ji kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin

cri
Yau 22 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin na fata da maraba da kasashen duniya da su fi bayar da tantuna a yayin da suke ba da agaji.

Mr. Qin Gang ya yi wannan bayani ne a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayar a wannan rana. Inda ya ce, bisa hakikanin halin da yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan ke ciki, yanzu kasar Sin na bukatar tantuna fiye da miliyan 3.3, amma yanzu tantunan da ake iya gabatarwa ga yankuna masu fama da bala'in sun kai dubu 400 kawai.

Bayan haka kuma, Mr. Qin Gang ya bayyana cewa, tun bayan da aka samu girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, kasar Sin ta samu goyon baya sosai daga kasashen duniya. Kasashe da yawa sun gabatar da taimako da kungiyoyin ceto da na likitanci zuwa kasar Sin, kasar Sin kuma za ta yi la'akari da wannan bisa bukatun yunkurin ceto, da kuma karfin karbi na wurin. Kasar Sin na kara yin godiya sosai ga taimakon da kasashen duniya suka bayar. (Bilkisu)