Amma duk da haka, a yayin da kafofin yada labarai na duniya ke nuna yabo a kan yadda gwamnatin Sin ke ba da agaji, wasu kafofin yada labarai suna ganin cewa, yadda gwamnatin kasar Sin ta dauka matakai cikin hanzari ya kasance matsayi kawai da ta dauka domin kusantowar wasannin Olympics, har ma wasu kafofin yada labarai sun bayyana mamakinsu.
A kasashen yammaci, akwai wani karin maganar da ke cewa, "ba a gina Rome cikin kwana daya ba". To, hakan nan ma yadda gwamnatin kasar Sin ta ba da agaji cikin hanzari da inganci da kuma irin kwarin gwiwa da ta nuna ba su fito cikin dare daya ba, su wani bangare kawai daga cikin irin sauye-sauyen da ake samu a kasar Sin.
1 2 3 4
|