|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-05-22 20:56:00
|
|
(Sabunta) Mutane 51151 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan
cri
Bisa rahoton da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar an ce, ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 10, mutane 51151 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane 288431 suka ji rauni, sannan 29328 suka bace. Ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi daga gida da waje da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 21.416.
Bayan haka kuma, ma'akatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayar da rahoto cewa, ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 12, mutanen da ake yi masu jiyya a asibitoci sun wuce 68600, har zuwa yanzu kuma, akwai mutanen da yawansu ya kai sama da 33600 suna asibitoci.
Bisa rahoton da ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta bayar an ce, ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 2 na yamma, kananan kukumomi na kasar sun bayar da kudin Sin RMB biliyan 13.975, don yaki da bala'in girgizar kasa. (Bilkisu)
|
|
|