Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 17:32:39    
Bankin ADB tana kokarin ba da taimako ga kasashen Afirka domin tinkarar matsalar karancin hatsi

cri

Yayin da ake fuskancin matsanancin karancin hatsi a kasashen Afirka, bankin ADB wanda ya zama hukumar kudi mafi girma da ke tsakanin gwamnatocin kasashen Afirka yana kokarin daukar matakai a jere domin ba da taimako ga kasashen Afirka wajen tinkarar matsalar karancin hatsi.

A kwanakin baya, Mr. Donald Kaberuka shugaban bankin ADB ya nuna cewa, yanzu farashin hatsi yana karuwa, kuma farashin taki da sufuri yana karuwa, saboda haka, sha'anin noma na kasashen Afirka yana bukatar kasashen duniya su kara ba da taimako.

Saboda mummunan tasiri, kamar karuwar bukatun hatsi, da raguwar yawan hatsi da aka samu sabo da mummunan yanayi, da karuwar yawan hatsi da aka kashe domin kirkirar makamashi, da ayyukan baranda, a cikin watannin baya, farashin hatsi na kasashen duniya yana ta karuwa sosai, wannan ya haifar da matsanancin tasiri ga kasashen Afirka, musamman ma ga kasashe mafi tallauci. Bisa kididdigar da bankin ADB ya yi, a cikin watannin baya, farasin shinkafa na kasashen duniya ya riga ya karu daga dolar Amurka 373 zuwa dolar Amurka 760 na ko nauyin Ton guda, kuma farashin masara mai zaki ya karu daga dolar Amurka 171 zuwa dolar Amurka 220 na ko nauyin Ton guda.

A kwanakin baya, a cikin taron shekara shekara da bankin ADB ya yi a Maputo babban birnin kasar Mozambique, an yanke shawarar kafa wani asusun taki wanda zai gabatar da kudin rangwame ga manoman kasashen Afirka, ta haka domin ba da taimako gare su wajen tinkarar karuwar farashin taki. Bankin ADB yana fatan zai iya tarar kudin dolar Amurka miliyan 500 a cikin watanni 6 masu zuwa ga asusun taki.

Mr. Kaberuka ya nuna cewa, asusun taki yana bukatar a tara kudi daga jama'a, kuma yana bukatar taimakon daga kasashen duniya. Ya ce, farashin taki ya karu daga dolar Amurka 245 a watan Janairu zuwa dolar Amurka 1100 a watan Afrilu na ko wane Ton guda.

A farkon wannan wata, bayan taron da majalisar bankin ADB ta yi a kasar Tunisiya, an sanar da cewa, bankin zai sake samar da rancen kudin taimako na dolar Amurka biliyan guda domin taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar matsalar karuwar farashin hatsi. Bayan haka, yawan kudin rancen taimako da bankin ADB ya samar ga sha'anin noma na kasashen Afirka ya kai dolar Amurka biliyan 4.8.

Ban da haka kuma, Mr. Kaberuka ya nuna cewa, bankin ADB zai ba da taimako ga gwamnatocin kasashen Afirka kan manyan gine-gine, ta haka domin tabbatar da manoma za su iya kai amfanin gona zuwa kasuwanni cikin lokaci. Ya ce, saboda manyan gine-gine marasa suna baya bayacigaba, manoma ba su iya kai amfanin gona zuwa kasuwanni, kasashen Afirka sun bata hatsi da yawa.

Kasar Liberia ta riga ta sanar da umurnin hana fitar da hatsi domin tinkarar karuwar farashin hatsi. Ban da haka kuma, wasu kasashen Afirka kamar Malawi su ma sun dauki matakai kamar haka. Mr. Kaberuka ya yi nuni da cewa, dole ne kasashen Afirka suna kawar da umurnin da suke daukawa don hana fitar da hatsi, saboda wannan zai tsananta mummunan halin da ake ciki, kuma zai bata moriya na bangarori dabam daban.

Bisa kididdigar da bankin ADB ya yi, yanzu a kasashen Afirka, akwai mutane fiye da miliyan 100 suna fuskantar babbar barazana ta karuwar farashin hatsi. Yanzu yawan rashin hatsi ya kai Ton miliyan 36 a kasashen Afirka. A kasashen Guinea, da Gambia, da Djibout, da Masar, da Sudan, da Chad da sauran kasashe 6 suna cikin mummunan hali saboda matsalar karuwar farashin hatsi.

Yanzu, ban da bankin ADB, hukumomin da abin ya shafa na majalisar dinkin duniya, da bankin duniya, da bankin raya tattalin arziki na Asiya da sauran kungiyoyin kasa da kasa suna dauki matakai domin ba da taimako ga kasashen da ke fama da matsalar karuwar farashin hatsi.