A ran 21 ga 22 ga wata, wasu shugabannin kasa da kasa sun je ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashensu, domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa a gundumar Wenchuan.
Jiya 21 ga wata, shugba Umaru Musa Yar'adua na kasar Nijeriya tare da matarsa sun tafi ofishin jakadancin Sin a Nijeriya domin nuna ta'aziyya ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon bala'in girgizar kasa. Haka kuma, shugaba Yar'adua ya sanar da cewar, zai bayarwa kasar Sin tallafin dala miliyan 2 wajen yaki da bala'in da ceto mutane.
Ban da shi kuma, a ran 21 ga wata, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Cuba Mr. Raul Castro, da kuma ministar harkokin waje ta kasar Iceland Madam Ingijorg Solrun, da firayin ministan kasar Hungary Mr. Gyurcsany Ferenc, da firayin ministan kasar Czeck Mr. Mirek Topolanek, da kuma mataimakin shugaban kasar Brazil Mr. Jose Alencar, da shugaban majalisar wakilai ta kasar Mr. Arlindo Chinaglia sun nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa.(Danladi)
|