Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 16:09:56    
An soma bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Bejing a Ningbo

cri

An cigaba da zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing yau 22 ga wata a birnin Ningbo na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin.

Domin nuna babban alhini ga mutane wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa yankin Wenchuan na lardin Sichuan, an dakatar da bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing har ranaiku 3 daga ranar 19 ga wata zuwa ranar 21 ga wata bayan da aka yi shawarwari tare da kwamitin gasar wasannin Olympics na kasa da kasa. Da karfe 7 da safiyar yau din nan ne, aka cigaba da yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing. An kaddamar da bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a tashar jiragen ruwa ta Beilun a birnin Ningbo.

Gaba daya ne akwai mutane masu dauke da fitila guda 118 wadanda suka halarci bikin. Sun shafe kimanin awoyi 6 da minti 15 suna zagayawa da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing, tsawon hanyar da aka ratsa da fitilar ya kai kilomita kimanin 12.8. Yau da maraice, za'a shirya bikin yawo da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Jiaxing na lardin Zhejiang.(Murtala)