Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 15:35:46    
Wasu shugabannin kasashen duniya da na kungiyoyin duniya sun yabawa ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane da kasar Sin take yi

cri
A cikin 'yan kwanakin nan, wasu shugabannin kasashen duniya sun tafi ofishin jakadanci da karamin ofishin jakadanci na kasar Sin dake ketare, da sakateriyar Sin dake kungiyoyin kasa da kasa, domin nuna ta'aziyya ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa Wenchuan ta lardin Sichuan, da jinjinawa gwamnatin kasar Sin wajen tafiyar da ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane.

Jiya 21 ga wata, shugba Umaru Musa Yar'adua na kasar Nijeriya tare da matarsa sun tafi ofishin jakadancin Sin a Nijeriya domin nuna ta'aziyya ga mutane wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon bala'in girgizar kasa. Haka kuma, shugaba Yar'adua ya sanar da cewar, zai bayarwa kasar Sin tallafin dala miliyan 2 wajen yaki da bala'in da ceto mutane. Ya kuma nuna babban yabo ga irin ayyukan cude-ni-in-cude-ka da jama'ar Sin suke yi, da cikakkiyar jaruntaka da suke nunawa yayin da suke kokarin yaki da mummunan bala'in girgizar kasa da ceto mutane.

Kazalika, shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya ce, gwamnatin kasar Sin tana maida hankalinta sosai kan zaman rayuwar jama'a, kuma tana daukar aikin ceto mutane a gaban kome, da kokarin ceto mutane ta hanyar kimiyya.

A waje daya kuma, firaminista Abdelaziz Belkhadem na kasar Aljeriya ya yi nuni da cewar, bisa gudummowar da gamayyar kasa da kasa suka bayar, gwamnatin kasar Sin za ta samu galaba kan mummunan tasirin da bala'in girgizar kasa ya haifar.

Dadin dadawa kuma, shugabannin kasashen Japan, da Sri Lanka, da Columbia, da Malaysia, da Morocco, da Ukraine, da Czeck, da Brazil, tare kuma da jami'an ofishin MDD dake Vienna da na hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa sun nuna babban yabo ga matukar kokarin da gwamnatin kasa Sin take yi wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceto mutane.(Murtala)