Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-22 14:37:13    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin (F)

cri

Muuwar aure abin takaici ne ga maza.

Mr Mao ya sha wahala yayin da ya je ofishin yin rajistar aure na birnin Beijing a watan jiya.Mr Mao yana cikin wannan ofishin ba domin yin rajistar aure ba akasin haka yana neman kashe aurensa da mata. Wani abin takaici ya same shi shi ne kamata ya yi ya karanta sanarwar yin rabuwar aure a fili. Mr Mao ya ce " Idan ba na karanta wannan sanarwar, ofishin bai ba ni iznin yin rabuwar aure ba.

Mr Mao ya ce " mutuwar aurensa abu ne da ya girgiza masa zuciya. Karanta sanarwar ya kara tsananta masa bakin cikin da ya ke fama da shi. Ban sani ba me ya sa aka kafa wannan ka'ida da ya kamata a bi yayin da ake yin rabuwar aure."

Wannan ka'idar da ake bi ba a birnin Beijing kawai ba, duk wanda ya ke neman yin rabuwar aure da radinsa a birane kamar Nanchang da Shanghai da kuma Nanjing ya karanta irin sanarwar wadda a ciki an tanadi matsayinsa da ranar yin aure da dalilin yin rabuwa.

Ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta tsaida wannan ka'ida ne duk domin fadakar da mutanen da ke neman yin rabuwar aure duk da haka mutane da yawa suna adawa da wannan ka'ida da cewa azaba ce ga masu neman yin rabuwar aure.

Ma'aikatar kula da harkokin jama'a tana mai ra'ayin cewa aka kafa wannan ka'ida ne duk domin kare wadanda ba su iya kare hakkinsu ba yayin da ake yin rabuwar aure, kamar wadansu mutanen da ke fama da matsalolin hankali. Wani ma'aikacin dake cikin ofishin ya ce " yayin da ake karanta sanarwar ma'aikatan ofishin su iya duba yadda suka karanta da yi musu tambayoyi domin gane ko wane ne daga cikin su biyu yana neman yin rabuwar aure da radinsa ko ba shi da nufin yin rabuwar aure da radinsa ba.Daga bisani za a yanke hukunci mai daidaici kan wadanda batu ya shafa."

"Ban da wannan kuma,an yi wannan biki ne domin fakadar da masu neman yin rabuwar aure kan amfanin takardun shaida da ikonsu da kuma hakkinsu bayan mutuwar aure."

Mr Zhu Liyu,wani lauya ne da ya kammala karatunsa a jami'ar Renming ya bayyana cewa dalili nan ba shi da ma'ana. Ya ce kashe aure da yin aure sun sha banban da juna sosai. Miji da mata ba su da nauyin kan juna bayan mutuwar aure.

Wani masani ilimin dokoki,Mr Qiu Lufeng dake cikin Jami'ar Nanjing ya bayyana cewa karanta sanarwar yin rabuwar aure ya sanya ofishin yin rajistar aure da ya yi gudun nauyi bisa dokoki.

Bayan da suka karanta sanarwar yin rabuwar aure da sa sunayensu a kan takardar shaida, masu neman kashe aure su kansu sun dauki nauyi kan mutuwar aurensu ba ofishin yin rajistar aure ba ne ya dau nauyi kan mutuwar aure ba. Ya kuma gaya wa ma'aikatan ofishin da su bukaci masu neman kashe aure da su karanta sanarwar da babbar murya, kuma sun yi musu tambayoyi domin su gane abin da aka rubuta a kan takardar shaida. Ya kuma yi kira ga mutanen kasa da su kara mayar da hankalinsu kan mutanen da ke fama da matsaloli na hankali.(Ali)