Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-26 08:49:54    
Karamin rancen kudi ya taimaka wa marasa aikin yi samun guraban aiki

cri

Kafin shekaru uku mace mai suna Jin Qilei da Song Lihong aka sallame su daga masana'anta. Bayan da suka rasa aikin yi, sun fara shan wahala a cikin zama. Bayan da suka samu rancen kudi na kudin Sin RMB Yuan dubu ashirin, zamansu na kara kyautatuwa,suna fatan samun babban ci gaba. Kamar su biyu,sauran marasa aikin yi da yawa a birnin Qiqihar na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabacin kasar Sin sun sake samo dabarun zama da kuma sabuwar alkibla, sun kafa wani workshop na yi wa zane ado.

Da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya shiga wani gidan mazauna wurin a yankin Tiefeng dake a birnin Qiqihar, kayayyakin fasaha da aka yi musu ado mai kyaun gani wadanda aka rataya kan jikin bango sun dauke hankalinsa. Da ya shiga ciki, ya ga mata shida ko bakwai su zauna a kewayen wani babban tebur,dauke da allura da zare, suna yi wa zane ado iri iri bisa fasalin da aka tsara, wannan karamin workshop ne da ya shahara a birnin saboda kayayyakin fasaha masu cin ado mai kyaun gani da ya fitar.

Mai kafa workshop din ita ce Jin Qilei. Kafin shekaru uku, tana daya daga cikin marasa aikin yi dubu 120 na birnin Qiqihar saboda aka yi wa masana'antu kwaskwarima bisa tsare tsaren hannayen jari. Matsin lamban zaman rayuwa ya tilasta Jin Qilei ta yi dogon tunani da kokarin samun aikin yi. A da Jin Qilei ta taba aiki a fannin yi wa zane ado, ita ma tana sha'awar kayayyakin ado ainun. Shi ya sa ta tafi birnin Suzho dake kudancin kasar Sin wanda ya fi shahara wajen yin kayan ado a kasa ta samu horo na watanni uku, to koma wurin da take zama.

Ta ce "Bayan da aka sallame ni,samun aikin da ya dace da ni ba aiki mai sauki ba ne, ina so in kinkintsa wasu 'yan mata mu yi wa zane ado domin ina son kayan ado sosai,wannan kuma fasahar al'ada ce ta al'ummar kasar Sin. Tare da wannana dabara, mun fara aikin sannu a hankali.A cikin yunkurin da muka yi na bude wannan karamin workshop, mun samu cikakken goyon baya daga gwamnatoci na mataki daban daban a yankin Tiefeng."

Kamar yadda sauran birane na kasar Sin suke, birnin Qiqihar ya fuskanci matsin lamban yawan marasa aikin yi da aka samu saboda kwaskwariman da aka yi wa masana'antu bisa sabbin tsare tsare cikin shekarun baya. Kowace shekara ana bukatar gwamnatin birnin Qiqihar da ta sake samar da guraban aikin yi ga ma'aikatan dubu 120 da aka sallame su, ciki har da ma'aikatan da suka samu aikin yi a shekarar bara,a wannan shekara aka sake sallame su,da ya kamata a sake samar da aikin yi zuwa gare su. Ban da wannan kuma sabbin leburori dubu 25 da aka samu a kowace shekara suna bukatar aikin yi. Bisa wannan hali mai tsananin da take ciki, gwamnatin birnin Qiqihar ta niyyata canza hanyar da take bi a da wajen samar da aikin yi, ta kawo sabuwar shawarar samar da guraban aikin yi ta hanyar bude sabbin sana'o'I, ta kuma dauki matakan takameme na gaggauta bunkasa sana'o'i. mataimakin shugaban hukumar kula da kwadago ta birnin Qiqihar Mr Zhao Qien ya ce, "Matakai uku ne muka dauka, na farko mun ba da horo ga marasa aikin yi ta yadda za su kara kwarewarsu wajen aiki. Na biyu, mun ba da taimako ta hanyar tsara manufa, mun ba da taimakon kudi ga wadanda suka kafa sana'o'I, na uku mun ba da jagoranci da hidima ga wadanda suka kafa sana'o'I, da kago wani yanayin goyon baya da kulawa ga masu kafa sana'o'i. mun kafa wani sashen kula da wadanda suka kafa sana'o'I da kungiyar kwararru."

Domin warware manyan matsalolin da masu kafa sana'o'I su kan yi fama da su a fannin kudi na kaddamar da shirye-shiryensu, bisa jagorancin magajin gari na birnin, ma'aikatun gwamnatin birnin Qiqihar suna goyon bayan marasa aikin yi da bayar da tabbaci wajen samun rancen kudi. Mataimakin shugaban hukumar kula da kwadago ta birnin Qiqihar Zhao Qiwen ya ci gaba da cewa,

"Matsala ta farko da ya kamata mu warware ita ce samar da karamin rancen kudi ga wadanda suka kafa sana'o'I domin marasa aikin yi su kan fama da karancin kudi wajen kafa sana'o'i. na biyu da wuya marasa aikin yi su samo wadanda za su bayar ta tabbaci wajen samun rancen kudi. Ya kamata masu ba da tabbaci suna da kudin shiga kowane wata. Da farko gwamnatin birnin ta yi kira ga ma'aikatansu da su hada kansu da marasa aikin yi da bayar da tabbaci zuwa gare su ta yadda su samu rancen kudi,ta kuma bukaci ma'aikatan gwamnatin da su ba da jagora da hidima ga marasa aikin yi a cikin yunkurinsu na kafa sabbin sana'o'i."

Bisa taimakon da manya da kanana na birnin suka baiwa marasa aikin yi a cikin yunkurinsu na kafa sana'o'I, Jin Qilei ta niyyata ta bude wani workshop na yi wa zane ado. Bisa tabbacin da madam Huang Yingge dake aiki a ofishin samar da tabbaci ga kwadago na yankin, Jin Qilei ta samu rancen kudi na kudin Sin RMB Yuan dubu ashirin. Madam Huang Yingge ta ce ta yi farin ciki da bayar da taimako ga Jin Qilei da ta bude workshop din na yi wa zane ado. Madam Huang Yingge ta ce,"A ganina Jin Qilei tana da iyawa. Ta yi amfani da wannan rancen kudi, ta tattara wasu mata su yi zane ado a gida,su samu kudi. Rancen kudi Yuan dubu 20 da ta samu bisa tabbacin da na bayar ya haifar da da mai ido, na yi farin ciki da ganin haka."

A cikin shekaru biyu da 'yan kai da suka shige bayan da aka bude workshop na yi wa zane ado, marasa aikin yi da suka zo wannan wurin domin neman aikin yi sai kara yawa suke. A da mata shida ko bakwai suna aiki a wannan workshop,amma a halin yanzu yawansu ya wuce metan, ciki ba marasa aikin yi na da kawai ba har ma da mutanen da suka sha wahalar zaman rayuwa kamar su nakasassu da wadanda suka yi ritaya da kuma masu kanana kudin shiga. Jin Qilei ta ce,

"Mun dauki wasu ma'aikatan da aka sallame su da nakasassu a matsayin aiki, ban da wannan kuma mun dauki wasu da suke sha'awar yi wa zane ado da masu ritaya,dukkansu sun wuce metan, a da suna aiki a masana'anta ko kamfanoni, daga baya sun koyi sana'ar yi wa zane ado. Samar da guraban aikin yi ga karin mata burina ne na yi abin da nake so,ina farin ciki da yin haka."

Madam Song Lihong ita ma'aikaciya ce da aka sallame ta daga wata masana'anta kafin ta zo workshop din da Jin Qilei ta kafa. bayan da ta rasa aikin yi, ba abun yi a gida sai kallon shirye shiryen talabiji a kowace rana, ba ta da hanyar samun kudi, ta kuma sha wuya cikin zama. Wata rana ba zato ta samu labarin daukar marasa aikin yi daga workshop din, nan da nan ta zo wurin ta samu aiki.Bisa jagorancin da Jin Qilei ta yi mata, ta fara koyon sana'ar yi wa zane ado. A cikin shekarun biyu da suka shige, bisa taimakon da sauran matan suka yi mata, ta kara kwarewarta sosai wajen yi wa zane ado, har ta zama malamar koyarwa ga sauran mata. Madam Song Lihong ta samu abubuwa da dama a cikin shekaru biyu na baya.

Ta ce" shekaru biyu da suka shige ba ni da aikin yi, na sha wahala wajen saye abubuwa. Bayan shekarun nan biyu,kudin da na samu ya karu, yanzu ina jin dadin zama. Da na kammala aikin yi wa wani zane ado,ina jin in samun ci gaba. Na koyi fasahar yi wa zane ado,wannan fasaha za ta taimake ni a duk rayuwata,ba zan yi watsi da ita ba har abada. Ban da wannan kuma zan iya ba da taimako ga sauran 'yanuwa mata."Bisa labarin da aka bayar, an ce dukkan matan da suka daddale kwangiloli da workshop din yi wa zane ado,suna iya yi wa zane ado a gidajensu, bayan da suka kammala,su kai kayan da suka yi wa ado a workshop. A yanzu ana sayar da kayayyakin da wadannan mata suka yi musu ado zuwa kasashen Rasha da Korea ta arewa da kuma Australiya.

Da aka juya kan nasarar da workshop din ya samu, madam Li Jiulan wadda tana da shekaru 67 da haihuwa ta fara koyon fasahar yi wa zane ado bayan da ta yi ritaya,ta yi aiki a fannin makanikanci ne a da. ta ce Madam Jin Qilei ta mai da hankalinta sosai kan ingancin kayayyakin da aka yi musu ado, a sa'I daya kuma ta nuna girmamawa da sa kulawa ga matan da ke aiki domin workshop dinta shi ya sa workshop ya cike da fara'a da farin ciki. Da ya ke ta tsufa, ba ta kai matsayin yadda 'yan mata suka yi wa zane ado ba, ta kan nitsu wajen nazarin fasaha da kare kwarewarta wajen yi wa kayayyaki ado.(Ali)