Ran 21 ga wata, a nan birnin Beijing, ministan harkokin jama'a na kasar Sin Mr Li Xueju ya jaddada cewa, yanzu hukumomi daban daban na harkokin jama'a na yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa suna ci gaba da mayar da aikin tsugunar da mutane gaban kome, don farfado da zaman oda da doka yadda ya kamata a wurin, haka kuma ya kamata a yi iyakacin kokari don ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'ar da bala'in girgizar kasa ta ritsa da su.
A gun taron da ma'aikatar harkokin jama'a ta yi kan tallafawa wuraren da bala'in girgizar kasa ya shafa ta Video, Li Xueju ya bayyana cewa, dole ne ma'aikatar harkokin jama'a ta yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa su dauki hakikanan matakai don tsauganar da jama'a a wurin, da gudanar da ayyukan rarraba abinci da kudaden alawus da abubuwan zaman rayuwa ga mutane da girgizar kasa ta rutsa da su da warware matsalar wajen wuraren kwana da abinci da tufafi da ganin likita.(Bako)
|