A ran 21 ga wata da safe a ofishin kula da harkokin waje na ma'aikatar tsaron kasar Sin, hafsoshin soja 61 da suka zo daga ofisoshin jakadanci na kasashen 47 da ke kasar Sin sun saurari bayanin da aka bayar kan yadda sojojin 'yantar da jama'ar Sin da rundunar sojoji 'yan sanda suke yin ceto da kau da bala'in girgizar kasa, kuma sun yaba sojojin kasar Sin bisa kokarin aikin da suke yi wajen ceto da kau da bala'in.
A gun taron, sassan da abin ya shafa na sojojin 'yantar da jama'a da na 'yan sanda sun yi bayani ga hafsoshin soja a ofisoshin jakada da ke kasar Sin kan muhimman tsare-tsare da ayyukan da suke gudana da kuma ayyukan bajinta suke yi wajen aikin ceto da kau da bala'in girgizar kasa, kuma sun amsa tambayoyin da wadannan hafsunan soja suka yi musu kan matsalolin da suke jawo hankulansu. Yayin da wasu hafsunan soja a ofisoshin jakadanci ke kasar Sin suke amsa tambayoyin da manema labaru na kamfanin Xinhua na kasar Sin suka yi musu sun bayyana cewa, a gun wannan aikin ceto da kau da bala'in girgizar kasa da ake yi, sojojin kasar Sin sun yi fifitattun ayyuka, ayyukan da suka yi cikin gaggauwa da bajinta sun ba wa mutane zurfaffiyar alama. (Umaru)
|