A ran 21 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya nanata cewa, a halin yanzu ya kamata daga wani gefe a yi aikin ceto don kau da bala'in girgizar kasa, daga gefe daban kuma a tsaya haikan ga bunkasa tattalin arzikin kasar.
A wannan rana kuma Mr. Wen Jiabao ya shugabanci taron harkokin yau da kullum na majalisar gudanarwa ta kasar Sin don yin bincike da kuma tsara shirin aikin aikin ceto don kau da bala'in girgizar kasa, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.
Taron ya nanata cewa, ya kamata a yi matukar kokari ga yin aikin ceto don kau da bala'in girgizar kasa, kuma a ci gaba da ceci mutane da ke karkashin kangaye, kuma a yi jigilar masu jin rauni zuwa asibitocin da ke da sharuda masu kyau wajen likitanci, da karfafa aikin rigakafin cututtuka. Kuma ya kamata a zaunar da jama'a masu fama da bala'in da kyau don samun tabbaci gare su wajen abinci da sutura da ruwan sha mai tsabta da gidajen kwana masu inganci. Kuma ya kamata a gyara manyan gine-gine da suka lalace sabo da girgizar kasa, kada a kai musu sabon illa. Kuma a tsara shirin farfado da aikin kawo albarka da zaman rayuwa tun da wuri. (Umaru)
|