Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 22:12:31    
Sin na fatan kasashen duniya za su fi bayar da tantuna a yayin da suke ba da agaji

cri
Yau 21 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Mr. Qin Gang ya bayyana cewa, Sin na fatan kasashen duniya za su fi bayar da tantuna a yayin da suke bayar da agaji.

Mr.Qin Gang ya ce, kwanan baya, bayan da kasar Sin ta bayyana burinta na son samun taimakon tantuna daga gamayyar kasa da kasa, kasashe da kungiyoyi sun mayar da martani cikin hanzari, kuma sun samar wa kasar Sin tantuna da yawa. Sabo da haka, Sin ta nuna musu godiya.

Amma sabo da jama'ar da girgizar kasa ta galabaitar da su sun yi yawa, shi ya sa ana ci gaba da bukatar dimbin tantuna wajen tsugunar da su. Sabo da haka, Sin na fatan kasashen duniya za su fi ba da tantuna a yayin da suke ba da taimako.(Lubabatu)