Yau 21 da yamma, lokacin da aka shiga kwana ta uku na yin zaman makoki a kasar Sin, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta karbi dimbin wakilan MDD da jami'ai da jakadu na gwamnatocin kasashe daban daban da ke nan kasar Sin.
A madadin MDD ne, Khalid Malik, wani jami'in MDD da ke kasar Sin, ya bayar da kudaden agaji da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 8 ga yankunan da girgizar kasa ta shafa a lardin Sichuan.
Sa'an nan, a madadin gwamnatin Botswana ne, ministan ilmi da fasaha na kasar wanda ke yin ziyara a kasar Sin, ya bayar da kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan miliyan 1 da dubu 60 ga yankunan da girgizar kasar ta shafa. Ban da wannan, a madadin tawagar jakadun kungiyar raya kudancin Afirka da ke kasar Sin ne, jakadan kasar Zambia da ke kasar Sin ya bayar da kudin taimako da yawansu ya kai kudin Sin yuan dubu 100 ga yankunan da girgizar kasa ta shafa.
Wakilinmu ya sami labari daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin cewa, a ran 21 ga wata da sassafe, kayayyakin agaji da masarautar Hashemite ta Jordan ta bayar sun riga sun isa filin jiragen sama da ke birnin Chengdu. Sa'an nan, Italiya ta riga ta bayar da kudin agaji na Euro miliyan 1 da kayayyakin agaji da darajarsu ta kai Euro miliyan 1 da dubu 500 ga kasar Sin. Kayayyakin agaji na farko da kasar Ukraine ta bayar ma sun riga sun isa birnin Chengdu a yau da yamma. Ban da wannan, kungiyar likitocin kasar Japan ta isa birnin Chengdu tare da kayayyakin agaji na kimanin ton biyar a jiya 20 ga wata da dare. (Lubabatu)
|