Wakilinmu ya samu labari a ran 21 ga wata daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin cewa, kungiyoyi masu yin ceto wajen kiwon lafiya na kasar Sin sun riga sun isa dukkan gundumomin da girgizar kasa ta shafa.
Bisa kididdigar da sassan kiwon lafiya suka yi an ce, yawan mutanen da suke aikin ceto a lardin Sichuan wajen likitanci da kiwon lafiya ya wuce dubu 45, ban da wannan kuma ma'aikatar kiwon lafiya da sauran sassa sun aika da mutane wadanda yawansu ya kai kusan dubu 11 domin warkar da marasa lafiya da shawo kan cututtuka da sa ido kan batun kiwon lafiya.
Ya zuwa ran 21 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta aika da mutane fiye da 2000 wandada suka zo daga wurare daban- daban na duk kasar domin yin rigakafin cututtuka, idan an hada da mutane masu rigakafin cututtuka na lardin Sichuan, sai a gane cewa jimlar mutane masu rigakafin cututtuka da suke aiki a wuraren da bala'in girgizar kasa ta shafa ta wuce 5,250. Ya zuwa yanzu, babu rahoton da aka bayar daga wuraren da bala'in girgizar kasa ta shafa game da cututtuka masu yaduwa kuma masu tsanani da matsalolin da suka faru ba zato ba tsammanni a fannin kiaon lafiya. (Umaru)
|