Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 17:31:41    
(Sabunta) Kasashen duniya suna ci gaba da ba da gudummawa ga kasar Sin sabo da girgizar kasa da ta faru a kasar

cri
A kwanakin baya, kasashen duniya suna ci gaba da nuna jejeto ga kasar Sin ta hanyoyin daban-daban sabo da girgizar kasar da ta faru a lardin Sichuan na kasar, kuma sun ba da agaji don yin ceto da kau da bala'i.

Daga cikin wadanda suka nuna jajantawa ga shugaba Hu Jinto na kasar Sin har da shugaba Jose ramos-Horta na kasar East Timor.

Daga cikin wadanda suka nuna jajantawa ga shugaba Wu Banbguo na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma har da Anusaa Mwanamwambwa, shugaban majalisar kasa ta Zambiya, da Heng Samrin shugaban majalisar kasa ta Kambodia. Da Tolofuaivalelei Falemoe Leiataua, shugaban majalisar kafa dokoki ta kasar Samoa, da Teshome Toga, shugaban majalisar wakilan jama'a ta kasar Habasha.

Daga cikin wadanda suka nuna jajantawa ga firaminista Wen Jiabao na kasar Sin kuma har da firaminista Nader al-Zahabi na kasar Jordan, da firaminista Meles Zenawi na kasar Habasha, da firaminista Ehud Olmert na kasar Isra'ila.

Daga cikin wadanda suka nuna jajantawa ga Mr. Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin kuma har da Rohitha Bogollagama, ministan harkokin waje na kasar Sri Lanka, da Madam Zainab Hawa Bangura, ministar harkokin waje ta kasar Saliyo, da Hon. Wilkie Rasmussen, ministan harkokin waje na kasar Tsibiran Cookisland.

Ban da wannan kuma Mr. Leslie Ramsammy, shugaban babban taron kiwon lafiya na duniya, da Chungu Mwila, mukaddashin babban sakataren kungiyar kasuwannin tarayya ta kudu maso gabashin Afirka wato COMESA, da Madam Anna Tibaijuka, direktar zartaswa ta hukumar gidajen kwana ta M.D.D. da leonid Drachevsky, shugaban hukumar Rasha ta kwamitin sada zumunci da zaman lafiya da bunkasuwa tsakanin Sin da Rasha su masu sun nuna jejeto ga kasar Sin.

Daga cikin kasashe da kungiyoyin kasashen duniya wadanda suka ba da gudummawa ga kasar Sin har da gwamnatocin kasashen Belgium da Luxembourg da Jamus da Morocco da Korea ta kudu da Australiya da Jsmus da Italiya da Sa'udiya da Rasha.

Kasashen Slovakia da Byelorussia da Gabon su ma sun ba da gudummawa ga kasar Sin wajen kudi da kayayyaki. Ban da wannan kuma, masana'antun kasar Amurka sun ba da taimakon kudi da na kayayyaki wadanda darajarsu ta kai kusan dala miliyan 30, kuma sun aika da wadannan kudi da kayayyaki zuwa shiyyoyi masu fama da bala'in ta hanyoyi daban-daban. (Umaru)