Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 16:32:12    
Sin za ta bada tallafi ga mutanen da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su a Wenchuan wajen zaman rayuwarsu na yau da kullum

cri
Yanzu haka a kasar Sin, akwai mutane sama da miliyan 5 wadanda suka rasa matsugunninsu a sanadiyyar mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa Wenchuan ta lardin Sichuan. Kasar Sin za ta tallafawa mutanen da bala'in ya rutsa da su wajen zaman rayuwarsu na yau da kullum.

Wakilinmu ya samo labari daga wajen ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin yau 21 ga wata cewar, ma'aikatar za ta samar da kudin alawus da abincin agaji ga mutanen yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa, ciki har da Sichuan, da Shanxi, da Gansu, da Chongqing, da Yunnan. Kowane mutum zai samu kudin alawus Yuan 10 da abinci rabin kilogiram a kowace rana cikin watanni 3. A waje daya kuma, marayu, da tsofaffin wadanda suke zaman kadaici, da nakasassu za su samu kudin alawus da yawansa ya kai Yuan 600 a kowane wata cikin watanni 3.

Domin bada tabbaci ga samar da wadannan kayayyakin agaji yadda ya kamata, ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta bukaci sassan da abin ya shafa da su inganta ayyukan sa ido kan samar da kudin alawus da abincin agaji ga mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su. Ya kamata a yanke hukunci ga wadanda suka karya ka'idoji daidai bisa doka.(Murtala)