Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 15:17:05    
Mr. Janusz Tatera da iyalinsa suna son gasar wasanni

cri

Mr. Tatera ya ji alfahari ya gaya wa wakilinmu cewa, Beijing da shi sun kulla kauna a tsakaninsu a yayin da Beijing ke neman samun damar shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, a ganinsa, shi ne mutum na farko da ya taya wa Beijing murnar cin nasarar samun damar shirya taron wasannin Olympic na Beijing.

A matsayinsa na babban sakataren kwamitin wasan Olympic na Poland, Mr. Tatera tare da sauran jami'an Poland sun halarci cikakken taron da kwamitin wasan Olympic na duniya ya yi a birnin Moscow a watan Yuli na shekarar 2001. A ran 13 ga watan Yuni na shekara 2001 da dare, kafin tsohon shugaban kwamitin Mr. Juan Antonio Samaranchi ya sanar da wace kasa ce ta sami damar shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, Mr, Tatera ya zauna tare da wasu jami'an kungiyar wakilai ta Beijing mai kula da neman samun damar shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Kamar yadda ya faru a yanzu, Mr. Tatera ya waiwayi abubuwan da suka auku a lokacin can da Sinawa kimanin biliyan 1.3 suka ji matukar farin ciki. Ya ce,

'Ban san Beijing zai ci nasara ko a'a ba, amma bayanin da jami'an Beijing ya yi a karshe ya burge ni sosai. Ina tsammani cewa, ana sa ran sosai cewa, Beijing za ta sami wannan dama. A lokacin can, ana gudanar da dukkan abubuwa yadda ya kamata. A yayin da shugaba Samaranchi ya sanar da cewa, Beijing za ta shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, na yi musafaha da jami'an kasar Sin don taya su murna.'

Game da dalilin da ya sa iyalinsa ya shiga aikin daukar iyalan wasan Olympic daga duk duniya, Mr. Tatera ya ce, taron wasannin Olympic na Beijing ya jawo hankulan mutane kwarai da gaske, yanzu mutane da yawa suna alla-alla zuwa kasar Sin da Beijing, iyalinsa na zaune a Beijing, babu tantama sun yi dabara don shiga yunkurin gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing.

Mr Tatera da iyalinsa sun taba shiga taron wasannin Olympic har sau 6, su ne iyalin wasan Olympic na zalla. Matarsa madam Tatera ta waiwaya cewa,

'Ko wane taron wasannin Olympic ya sha bamban da juna. Amma birnin Atlanta ya fi burge ni. Shi ne taron wasannin Olympic na farko da iyalina muka halarta. A lokacin can 'yata ta kai shekaru 11 da haihuwa kawai, ta je biranen Chicago da Atlanta tare da mu, ta kuma taimaki kungiyar wakilan Poland wajen yin ayyukan gabatarwa. Ko da yake ba mu kalli dukkan gasanni ba, amma mun fahimci yanayin musamman na taron wasannin Olympic sosai.'

Irin kyakkyawar fasahar da ta samu a lokacin yarantakarta ta ba da tasiri mai kyau ga Beata Tatera, 'yar Mr. Tatera. Yanzu wannan budurwa mai shekaru 22 da haihuwa tana karatu a Beijing, ta iya Sinanci sosai, tana neman zama mai aikin sa kai na taron wasannin Olympic na Beijing. Ta ce,

'Kullum abokaina da yawa su kan tambaye ni yaya Beijing take, suna fatan za su zo kasar Sin. Ina fatan zan bai wa bakin duk duniya tallafi a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic na Beijing.'