Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-21 12:14:26    
Ana bukatar tantuna cikin gaggawa domin tsugunar da fararen hula masu fama da girgizar kasa

cri
Yanzu mutane fiye da miliyan 5 sun rasa gadajensu sakamakon mumunar girgizar kasa da ta auku a gundunar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, yanzu yankuna masu fama da bala'in suna bukatar tuntuna cikin gaggawa domin tsugunar da fararen hula.

Jiang Li, mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin ya yi bayani a gun taron manema labarai da aka shirya a ran 20 ga wata, cewa yanzu ana tsugunar da yawancin fararen hula masu fama da bala'in ta hanyar dogaro da 'yan iyalinsu da abokansu, haka kuma an riga an bude kofar gine-gine da wuraren jama'a ciki har da hukumomin gwamnatocin wurin domin fararen hula masu fama da bala'i suke iya zama a ciki.

Kuma an labarta cewa, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta riga ta aika da tantuna dubu 280 zuwa yankuna masu fama da bala'in domin tsugunar da fararen hula masu fama da bala'in, amma ba su isa ba, ana bukatar tantuna cikin gaggawa. Yanzu ma'aikatar ta kara sayen tantuna dubu 700, kuma masana'antu suna kera su cikin gaggawa domin tura su zuwa yankuna masu fama da bala'in.(Kande Gao)