Ma'aikatar kudi ta gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin samar da kudin taimako Yuan 600 ga ko wane maraya da ko wane tsoho da kuma ko wane mutum nakasasshe da ya rasa dukkan 'yan iyali a cikin wannan girigrizar kasa da ta auku a lardin Sichuan na kasar Sin a ko wane wata domin tabbatar da zaman rayuwarsu.
Jiang Li, mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin ya yi bayani a gun taron manema labarai da aka shirya a ran 20 ga wata, cewa yanzu an riga an samu mutane 124 da ba su da 'yan iyali, ciki har da marayu fiye da 70 da kuma tsoffi da nakasassu fiye da 40. A nan gaba lardin Sichuan zai sake gina wasu gine-ginen jin dadin jama'a domin ciyar da wadannan mutane.(Kande Gao)
|