Daga ran 19 ga wata, Jama'ar da ke wurare daban-daban na kasar Sin suna bin hanyoyi daban-daban domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sabo da girgizar kasa da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, kuma suna yin addu'a don yin fatan alheri ga jama'ar da fama da bala'in.
A ran 19 ga wata a birnin Jincheng na lardin Shanxi, da binin Hangzhou na lardin Zhejing, mutanen birane sun yi nadin furanni da takarda, kuma sun sa furannin cikin ruwa, a birnin Shenzhen kuma, mutane sun daura kyallaye masu launin rawaya a hannayensu, sun yi haka ne duk domin yin addu'a ga mutanen da suka mutu, da yin fatan alheri ga mutanen da suke da rai.
A ran 19 ga wata da yamma da misalin karfe 2 da minti 28, shugabannin kasar Sin ciki har da Hu Jintao da Jiang Zeming da Wu Bangguo da Wen Jiabao dukkansu sun yi tsit tare da jama'a 'yan kabilu daban-daban na duk kasar domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa.
Ya zuwa karfe 6 na ran 20 ga wata da yamma, girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan ta yi sanadiyar mutuwar mutane 40,075, yayin da wasu mutane dubu 240 suka jikkata. Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tsai da cewa, kwanaki 3 wato daga ran 19 zuwa 21 ga wata za su zama ranakun zaman makoki.(Umaru)
|