A 'yan kwanakin baya, shugabannin kasa da kasa sun nuna tausayi da jejeto ga mutuwar mutane da yawa da kuma jin raunuka da yawa da kuma babbar hasara da kasar Sin ta samu sakamakon babbar girgizar kasa, sun yaba wa aikin ceto don yaki da bala'in girgizar kasa da kasar Sin ke yi.
A ran 19 ga wata da safe, shugaban kasar Peru Mr Alan Garcia ya je ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasarsa. Ya yaba wa aikin ceto da gwamnatin kasar Sin take gudanarwa cikin sauri, ya kuma yi imani cewa, kasar Sin za ta iya cin nasarar yaki da bala'in girgizar kasa, haka kuma za ta ci nasarar shirya gasar wasannin Olympics.
A ran 19 ga wata da safe, babban sakataren MDD Mr. Ban Ki-moon ya je wurin zaunaniyar tawagar kasar Sin dake MDD don nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu sakamakon bala'in, ya yabawa kasar Sin sabo da karfi da kasar Sin ke nuna lokacin da take fuskantar kalubalen. Ya yi imani cewa, tilas ne mutanen kasar Sin su warware matsalar nan da suke fuskantar bisa jagorancin gwamnatin kasar Sin.
A ran 20 ga wata da safe, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam, kuma mataimakin sakataren hukumar Jam'iyya ta sojoji ta kwamitin tsakiya, kuma ministan tsaron kasar Vietnam ya je ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasarsa, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar Sin.
Ban da wannan kuma, shugabannin kasar Korea ta arewa, da na Mongolia, da mataimakin shugaba na farko na kasar Peru, da kuma firayin minista da kuma ministoci 10 na kasar, da firayin ministan kasar Ecuatorial Guinea, da shugabannin majalisun dattawa da wakilai, da ministan harkokin waje na kasar Lebanon, da shugaban majalisar wakilai ta kasar Japan su ma sun mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sakamkon babbar girgizar kasa.(Danladi)
|