|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-05-20 21:48:45
|
|
Wajibi ne a dauki hakikanan matakai don magance bala'un da aka samu a sakamakon girgizar kasa, a cewar mataimakin firayin ministan kasar Sin
cri
A likacin da Mr. Hui Liangyu, mataimakin firayin ministan kasar Sin ke yin bincike kan halin bala'in girgizar kasa da lardin Sichuan ke ciki, ya nuna cewa, tilas ne a mayar da kwanciyar hankali ta jama'a a matsayin farko, kuma wajibi ne a dauki hakikanan matakai, don magance bala'un da aka samu a sakamakon girgizar kasa, ta yadda za a hana kara samun mutuwar mutane.
Bayan faruwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, an samu hadari a matarin ruwa da yawa, kuma a wasu wurare an samu bala'un zaizayewar duwatsu, da na kwararowar kasa, kazalika kuma an lalata wasu na'urorin fitar da adanan kayayyaki masu guba, da kuma bututun man fetur da na gas.
Mr. Hui Liangyu ya ce, a lokacin da ake magance bala'un da aka samu a sanadiyar girgizar kasa, a waje daya kuma, ya kamata a dauki hakikanan matakai, don tabbatar da kwanciyar hankali ta wadanda ke ayyukan ceto, da na likitanci, da kuma na sa kai. (Bilkisu)
|
|
|