Gwamnatin kasar Sin tana daukar matakai domin samar da kayayyaki da samun tabbaci ga zaman rayuwar jama'a masu fama da bala'in girgizar kasa da ke gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar.
A ran 20 ga wata wakilinmu ya samu labari daga wajen taron manema labaru da ofishin ba da labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya cewa, ya zuwa ran 20 ga wata da misalin karfe 12 na tsakar rana, gundumomi 8 masu fama da bala'in girgizar kasa mai tsanani da ke larfin Sichuan na kasar Sin suna ci gaba da yin mu'amala da sauran wurare ta hanyar waya ko internet. Farashin muhimman kayayyakin abinci ya yi daidai da na jajibere. Ya zuwa ran 20 ga wata da karfe 12 na tsakar rana, aikin ba da wutar lantarki da ake yi a lardin Sichuan da birnin Chongqing da lardin Gansu da na Shanxi yana tafiya yadda ya kamata.
Ya zuwa karfe 2 na ran 20 ga wata da yamma, jimlar kudin da gwamnatoci na matakai daban-daban suka ware domin yaki da bala'in girgizar kasa ta kai kudin Sin wato Yuan biliyan 11 da miliyan 727, yawan kudin taimakon aka samu daga sassa daban- daban na zaman al'umma kuma ya wuce Yuan biliyan 12.5. (Umaru)
|