Mun sami labari daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin cewa, ya zuwa karfe 9 na ran 19 ga wata da yamma, ba a sami rahoto game da manyan cututtuka masu yaduwa a shiyyoyi masu fama da babbar bala'in girgizar kasa da ta faru a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan da matsalolin da suka faru ba zato ba tsammani a fannin kiwon lafiya ba.
An ce, domin farfado da aikin ba da rahoto kan cututtuka masu yaduwa da matsalolin da suka faru ba zato ba tsammani a fannin kiwon lafiya a shiyyoyi masu fama da bala'in girgizar kasa mai tsanani dake lardin Sichuan tun da wuri, kafin lokacin farfado da tsarin ba da rahoto ta hanyar internet, an ba da rahoto kan cututtuka masu yaduwa da matsalolin da suka faru ba zato ba tsammani a fannin kiwon lafiya a shiyyoyi masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan ta hanyar wayar salula, kuma cikin kwanaki 10 masu zuwa za a ba da rahoto kan cututtuka masu yaduwa ta hanyar wayar a tsakanin mutane miliyan 10. (Umaru)
|