Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-20 20:39:28    
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya wakilci gwamnati da jama'ar kasar, don yin godiya ga kasashen duniya da su nuna juyayi da goyon baya kan bala'in girgizar kasa na Sichuan

cri
Yau 20 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang, ya bayyana cewa, bayan da aka samu girgizar kasa a Wenchuan na lardin Sichuan na kasar Sin, juyayi da goyon baya daga kasashen duniya, ba kawai sun bayar da taimako ga kasar Sin a fannin samar da kayayyaki ba, har ma sun kara kwarin gwiwa ga kasar Sin. Gwamnati da jama'ar kasar Sin sun yi godiya sosai kan wannan.

Ya zuwa yanzu, kasashe 166, da kungiyoyin kasashen duniya sama da 30, sun nuna juyayi ga kasar Sin, ofisoshin jakadanci na kasashen waje da ke nan kasar Sin, da kuma sassan wakilai na hukumomin kasashen duniya da ke kasar Sin, wadanda yawansu ya kai fiye da dari daya sun saukar da tutar kasa zuwa rabin sanda, don nuna jimami. Bayan haka kuma, kasashen Japan, da Rasha, da Korea ta kudu, da kuma Singapre sun aiko da kungiyoyin ceto na fasaha zuwa nan kasar Sin, kazalika kuma kasar Sin ta amince da kasashen Jamus, da Italy, da Rasha, da kuma Japan da su aika da kungiyoyin likitanci zuwa kasar. (Bilkisu)